1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta sassauta hanyar samun aiki a kasar

June 1, 2024

Sabon tsarin samun takardar visa ta shigowa Jamus ga masu neman aikinyi daga kasashen duniya da ba sa cikin kungiyar Tarayyar Turai ya fara aiki daga wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/4gWvt
Hoto: Gints Ivuskans/AFP

Tsarin na bukatar masu neman aikin su mallaki wani kati da aka yi wa lakabi da 'Chancenkarte. Hakan na nufin masu sha‘awar samun aiki a Jamus za su iya neman visa ba tare da mallakar aikin ba. Samun katin na Chancenkarte zai bai wa masu shi damar zuwa Jamus domin su jaraba neman aiki a cikin shekara daya.


Kwarewa a harshen Jamusanci ko Ingilishi da mallakar shaidar digiri ko shekaru biyu na kwarewa a fannin da mutum ke son samun aikin na daga cikin abubuwan da ake bukata kafin samun zuwa Jamus ta wannan hanya.


Wannan dai na cikin jerin matakai dabam-dabam da hukumomin Jamus suka dauka a baya-bayan nan domin tunkarar kalubalen rashin ma'aikata da kamfanonin kasar ke fuskanta.