1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta sallami jakadiyar Chadi dake kasarta

Binta Aliyu Zurmi
April 11, 2023

Jamus ta sanar da korar jakadiyar kasar Chadi a yau Talata, biyo bayan korar da gwamnatin rikon kwarya Chadi ta yi wa jakadansu a satin da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4Pv58
Mariam Ali Moussa
Hoto: Dean Calma/IAEA/Wikipedia

A ranar Juma'ar da ta gabata ce mahukuntan na Ndjemena suka bai wa jakadan Jamus Gordon Kircke sa'o'i 48 na ya bar kasar bisa zarginsa da rashin mutunta dokokin diplomasiyya.

Matakin da ya janyo daukar martani baiwa jakadiyar Chadi Mariam Ali Moussa kwanaki biyu na ta tatara inata-inata ta bar kasar.

A wata sanarwar da ma'aikatar harkokin kasashen ketaren Jamus ta wallafa a shafinta ta Twitter, ta bayyana takaicin korar jakadanta inda ta ce yana gudanar da aikinsa bil hakki da gaskiya.

Sanarwar ta kara da cewar za su ci gaba da tattaunawa da bangarorin biyu kuma har yanzu suna da sauran wasu kananan jam'ian diplomasiyyar su a kasar ta Chadi.