1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta nemi haɗin kan ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro

October 16, 2012

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jaddada anniyar ƙasar ta na ceto kuɗin Euro daga durƙushewa

https://p.dw.com/p/16R50
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firimiyan Sweden Fredrik Reinfeldt
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firimiyan Sweden Fredrik ReinfeldtHoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi ƙira da a samu ƙarfafa haɗin kai da tuntuɓar juna tsakanin ƙasashen dake amfani da kuɗin euro. Merkel ta yi wannan kiran kwanaki biyu gabanin taron ƙolin shugabannin ƙasashen da ke amfani da kiɗin euro. Da take jawabi tare da baƙonta firimiyan ƙasar Sweden Fredrik Reinfeldt, wanda yace yana duba yiwuwar shigar da ƙasashen da basa amfani da takardar kudin euro, su shiga shirin Merkel keutata hada-jhadar bankuna, inda za su haɗa hannu bisa tsarin tafiyar da bankuna.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita:       Mouhamad Awal