1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rundunar Jamus ta bar Afghanistan

Ramatu Garba Baba
June 30, 2021

A wannan Laraba rundunar sojin Jamus da aka jibge a kasar Afghanistan ke dawo wa gida bayan shafe shekaru 20 tana aikin tsaron kasar mai fama da tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/3vnnk
Afghanistaneinsatz der Bundeswehr endet
Hoto: Torsten Kraatz/Bundeswehr/dpa/picture alliance

Bayan shafe shekaru ashirin a kasar Afghanistan, a wannan Laraba rundunar da Jamus ta tsugunar a kasar za ta dawo gida. A yayin jawabinta, Ministar Ma'aikatar Tsaron Jamus, Annegret Kramp-Karrenbauer ta ce, rana ce mai cike da dimbin tarihi, bayan tarin kalubale da rundunar ta fuskanta a kokarin wanzar da zaman lafiya, a kasar da aiyukan mayakan Taliban suka hana kwanciyar hankali, ta kara da cewa, ba za a taba mantawa da sadaukarwar da sojojin suka yi ba, wasu sun rasa rayukansu wasu sun ji munanan rauni. 

Daga cikin rundunar sojin Jamus mai sojoji dubu daya da dari daya, kimanin (59) hamsin da tara ne suka kwanta dama. Tun bayan shelar soma janye rundunar kawance daga cikin Afghanistan, al'amurran tsaro suka soma tabarbarewa, rahotanni na cewa, mayakan Taliban sun karbe ikon yankuna (90) casa'in na kasar a tsukin soma aikin janye rundunar kawance.