Jamus ta kori wasu jami'an diflomasiya na Siriya
February 9, 2012Talla
Wannan kora dai ta zo ne bayan da jami'an tsaro na Jamus ɗin suka kama wasu mutane guɗa biyu suna yi wa wani jagoran yan adawar Siriyar da ke zaune a Jamus leƙen asiri.
Mutane guda biyu waɗanda ɗaya ɗan Jamus ne da kuma daya ɗan labanan babbar kotun kolin ƙasar da ke a karsruhe ta ce sun jima suna yi wa hukumar leƙen asirin ƙasar Siriya aikin. Haka kuma hukumar yan sanda ta kasar ta gudanar da bincike a gidajen wasu mutanen guda shida da ake zargi da lafin leƙen asirin yan adawar na ƙasar Siriya sai dai kuma babu wani a aka kama daga cikin su.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu