1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta haye zuwa zagayen quarterfinal

June 30, 2024

A ci gaba gasar cin kofin nahiyar Turai, mai masaukin baki Jamus ta doke kasar Denmark da ci biyu da nema da yammacin ranar Asabar.

https://p.dw.com/p/4hgc5
Dan wasan Jamus Jamal Musiala yana murnar zura kwallo
Dan wasan Jamus Jamal Musiala yana murnar zura kwalloHoto: Kenzo Tribouillard/AFP/Getty Images

Wasan da aka buga a birnin Dortmund, an tafi hutun rabin lokaci ne ba tare da samun wadda ta ci kwallo ba.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokacin ne kuwa, dan wasan Jamus Havertz ya zura wa Denmark a bugun fenariti.

Haka nan shi ma dan wasan tsakiya na Jamus din Jamal Musiala, ya kara wata kwallon, abin da ya bai wa kasar damar zuwa zagayen quarter-final

Ruwan sama da tsawa sun haddasa tsaiko na mintuna 35 jim kadan da farawa.

Yanzu dai Jamus na iya gamuwa da walau Spain ko kuma kasar Georgia a zagayen quarterfinal a birnin Stuttgart a ranar Juma'a.