1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramcin shiga Jamus ga wasu 'yan Saudiyya

Suleiman Babayo MNA
November 19, 2018

Gwamnatin Jamus ta haramta shiga kasar ga 'yan Saudiyya 18 da ake zargi da hannu kan kashe ficeccen dan jarida na Saudiyya Jamal Khashoggi a watan Oktoba da ya gabata.

https://p.dw.com/p/38W5J
Türkei Fall Khashoggi - Trauergebete
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/E. Gurel

Hukumomin Jamus sun haramta shiga kasar ga 'yan Saudiyya 18 da ake zargi suna da hannu wajen kashe dan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Samtanbul na Turkiyya. Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya tabbatar da haka a wannan Litinin a wajen taron kungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels na kasar Beljiyam.

Ranar biyu ga watan jiya na Oktoba aka hallaka Jamal Khashoggi, wanda ya kasance mai sukar Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarautar Saudiyya. Tun bayan faruwar lamarin masarautar Saudiyya ta shiga matsin lamba na kasashen duniya kan neman hukunta wadanda suke da hannu kan kisa gami da wanda ya ba da umurni, da ake kyautata zaton shi kansa Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarauta.