1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaJamus

Jamus ta habaka sabbin kayan binciken AI kan mulkin mallaka

Elizabeth Grenier, SB/MAB
August 13, 2024

Masu adana kayan tariri na tarayyar Jamus da suka tattara takardu da aka gaza tantancewa tun lokacin mulkin mallaka sun samu wata dama da taimakon "Kirkirarriyar Basira" wajen iya fahimtar abin da ke cikin bayanan.

https://p.dw.com/p/4jPhO
Katin waya daga Kamaru da ta kasance karkashin mulkin mallaka ta daular Jamus
Katin waya daga Kamaru da ta kasance karkashin mulkin mallaka ta daular Jamus Hoto: akg-images/picture alliance

Duk wanda yake bukatar yin wani nazari mai tasiri kan Jamus gabanin yakin duniya na biyu na bukatar kwarewa na musamman. Dole masu binciken su iya karanta rubutun hannun da ya bace baki daya daga harkokin yau da kullum na harshen Jamusanci. Wannan tsohon rubutun ya samo asali a lokacin zamanin da ya shude da Turawa ke neman ci gaba. Kana rubutun ya shahara a Jamus a shekarar 1911 inda aka koyar a makarantun Jamus daga shekarar 1915 zuwa 1941 har zuwa lokacin da 'yan Nazi suka haramta. Daga nan ne dalibai suka fara koyon rubutu irin na Ingilishi da ake amfani da shi har zuwa wannan lokaci.

Karin bayani: Yunƙurin ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin Kamaru da Jamus

Misalin rubutun hannu na wani basaraken Kamaru da aka yi amfani da fasahar AI wajen tantance shi
Misalin rubutun hannu na wani basaraken Kamaru da aka yi amfani da fasahar AI wajen tantance shiHoto: BArch/R 1001/5573/Image165/Bundesarchiv

Duk da Jamusawa sun ci gaba da amfani da rubutun har bayan yakin duniya na biyu, amma yanzu galibin Jamusawa ba sa fahimtar tsohon tsarin rubutun. Amma a yanzu da taimakon kirkirarriyar basira da masu adana kayan tarihi na Jamus suka taimaka aka samar za a iya sanin abin da rubuce-rubucen suka kunsa, inda ake da kundin bayanai kimanin 10,000 daga abubuwan da suka shafi manufofin Jamus lokacin mulkin mallaka.

Mulkin mallaka na Jamus ya fara daga karni na 19 wajen kame yankuna tare da kaddamar da yankunan zuwa na mallaka a Afirka da kudancin tekun Chaina. Mulkin mallaka na Jamus ya shafe tsawon shekaru 30 kacal daga shekarar 1884 zuwa karshen yakin duniya na Farko, amma duk da haka ta kasance ta uku wajen yawan yankunan mulkin mallaka bayan kasashen Birtaniya da Faransa. Sannan Jamusawa sun nuna rashin imani a zamanin mulkin mallaka.

Karin bayani: Rudolf Douala Manga Bell: Sarkin Kamaru da ya nuna turjiya ga Turawan mulkin mallaka na Jamus

Duala Manga Bell: Sarkin Douala da ya kalubalanci Jamusawa a Kamaru
Duala Manga Bell: Sarkin Douala da ya kalubalanci Jamusawa a KamaruHoto: Stadtarchiv Aalen/J. van Daalen

Wannan bayanan da yanzu aka samu fasahar da za a tattaro abin da suke ciki, ya kunshi babin tahirin Jamus mai cike da duhu, da yadda aka halaka sarakunan Doula lokacin mulkin mallaka a Kamaru. Kana da yadda aka aiwatar da kisan dare dangi kan kabilun Herero da Nama na kasar Namibiya a farkon karni na 20, wanda har sai zuwa shekara ta 2021 je Jamus ta amince da abin da ya faru a matsayin kisan kare dangi, da aka aiwatar a kasar ta Namibiya.