1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta fidda sanarwa kan Birtaniya

April 4, 2019

Jamus ta ce za ta bai wa 'yan Birtaniya, mazauna lokacin neman takardun zama a duk lokacin da Birtaniyar ta fice daga Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/3GDXI
Deutschland Ost-Ministerpräsidentenkonferenz
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Schutt

Fadar gwamnati da ke birnin Berlin ta ce za ta bai wa 'yan Birtaniya da iyalansu, da ke zaune a kasarta cikakken lokacin neman izinin zama a kasar, a duk lokacin da Birtaniyar ta kai ga raba gari da Tarayyar Turai.

A cewar ma'aikatar da ke kula da harkokin cikin gida, Jamus din za ta bai wa 'yan Birtaniya mazauna cikin nata ne watanni uku na farko, don cike takardun zama a kasar.

A ranar 12 ga wannan watan na Afrilu ne dai aka tsara Birtaniyar za ta raba garin nata da gamayyar kasashen na Turai.

A gefe guda kuwa, a ranar Laraba ne majalisar dokokin kasar ta amince da wani kudurin da zai sanya firaministar kasar Theresa May, neman karin wa'adi na ficewar kasar, bayan gaza cimma yarjejeniya kan batun na ficewa.