1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta dakatar da tallafin da take bayar wa ga UNRWA

January 28, 2024

Jamus ta bi sahun kasashen duniya da ke suka dakatar da tallafin da suke bai wa hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/4blFG
Shugaban hukumar UNRWA, Philippe Lazzarini
Shugaban hukumar UNRWA, Philippe Lazzarini Hoto: Salvatore Di Nolfi/picture alliance/KEYSTONE

Hakan dai na zuwa ne bayan da Isra'ila ta zargi cewa, ma'aikatan hukumar da dama ne aka gano suna da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Octoban bara. Gwamnatin Berlin ta ce ta dakatar da dukkannin wani tallafi da ta ke bayar wa ga hukumar har zuwa lokacin da za a kamalla bincike. Shugaban hukumar ta UNRWA, Philippe Lazzarini ya ce zargin ya shafi wasu takaitattaun ma'aikata ne, kana ya ce za a hukunta duk wanda aka kama da hannu cikin harin.

Sai dai ya nuna kaduwarsa kan dakatar da tallafin yana mai cewa,Falasdinawa a Zirin Gaza ba su cancanci wannan hukuncin na bai daya ba. A baya-bayan nan, dangantaka tsakanin Isra'ila da UNRWA na tsami sakamakon zargin da hukumar ke yiwa Isra'ilar na kai hari kan mafakar da ta ke bai wa 'yan gudun hijira.