1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta jingine hulda da kasar Nijar

Abdullahi Tanko Bala
July 31, 2023

Fadar gwamnatin Jamus a Berlin ta dakatar da dukkan tallafin kudi ga gwamnatin tarayyar Nijar har sai abin da hali ya yi.

https://p.dw.com/p/4UbVW
Niger Niamey | Proteste | Unterstützung der Militärputschisten
Hoto: AFP/Getty Images

Jamus na tuntubar takwarorinta da ke Nijar yayin da ta ke nazarin dammaki ga sojojinta da ke Nijar a halin yanzu da kuma janyewarta daga Mali a cewar ministan tsaron Jamus Boris Pistorius.

Ministan tsaron ya ce wadanda suka yi juyin mulki a Nijar sun yi alkawarin ci gaba da martaba yarjejeniyoyin kasa da kasa sai dai ya ce wannan abu ne da za a jira a gani.

A waje guda dai Jamus din ta sanar da dakatar da dukkan tallafin kudi da gudunmawar raya kasa ga Nijar sakamakon juyin mulkin. Ta kuma yi kashedin daukar wasu matakan bisa ga yadda al'amura za su wakana cikin 'yan kwanaki masu zuwa.