1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta bukaci tattanuwa da Rasha

Suleiman Babayo MAB
June 17, 2022

A hanyoyin neman kawo karshen yakin Ukraine, Shugaban gwamnatin Jamus ya bukaci ci gaba da tataunawa da shugaban Rasha.

https://p.dw.com/p/4CsQQ
Ukraine | Wolodymyr Selenskyj, Olaf Scholz und  Emmanuel Macron
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya bayyana muhimmanci ci gaba da bude hanyar sadarwa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha duk da ci gaba da kaddamar da yaki da Rasha ke yi kan kasar Ukraine, saboda tasirin sadarwar saboda irin yanayin da duniya ta samu kanta na yaki kamar yadda shugaban Faransa ke yi.

Scholz ya bayana haka lokacin hira da kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA, inda ya kara da cewa dole kasashen yammacin duniya su ci gaba da tattaunawa kan kokarin kawo karshen yakin da Putin ya kaddamar ranar 24 ga watan Febrairun wannan shekara ta 2022.

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da Firaminista Mario Draghi na Italiya gami da Shugaba Klaus Iohannis na Romaniya sun kai ziyara birnin Kiev na Ukraine bisa manufofin kawo karshen wannan yaki da ya haddasa tashin farashin kayan abinci a duniya.