1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta bukaci bahasi daga jakadan Koriya ta Arewa

Abdullahi Tanko Bala
October 23, 2024

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya kira babban jami'in diflomasiyyar Pyongyang a birnin Berlin game da rahotanni da ke cewa Koriya ta Arewa na tura sojoji zuwa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4m9Hz
Faretin sojojin Koriya ta Arewa
Hoto: Russian Defence Ministry/dpa/picture alliance

Jamus ta bukaci bayanai daga jami'in diflomasiyyar Koriya ta Arewa sakamakon karuwar damuwa na goyon bayan da Pyongyang ke bai wa Rasha a yakin da ta ke yi a Ukraine.

Idan har ta tabbata sojojin Koriya ta arewa suna cikin Ukraine kuma Koriya ta arewa na taimaka wa Rasha da sojoji a yakin, to hakan zai zama babban keta dokokin kasa da kasa kamar yadda ma'ikatar harkokin wajen Jamus ta wallafa a shafin sada zumunta na X

Taimakon da Koriya ta Arewa ke bai wa Rasha na barazana kai tsaye ga tsaron Jamus da kudirin zaman lafiya na tarayyar Turai.