1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Za a rika samun sakamakon gwajin corona cikin kwana 1

Binta Aliyu Zurmi
May 26, 2020

Jihar Bavaria da ke kudu maso yammacin kasar Jamus ta sanar da cewar sakamakon gwajin cutar corona da za a yi wa wadanda suka nuna alamun kamuwa da cutar zai iya samuwa cikin sa'o'i 24.

https://p.dw.com/p/3cmLM
Deutschland Berlin Pressekonferenz  Coronavirus | Markus Söder
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Wannan inji mahukuntan jihar na nufin mutane za su iya sanin ko suna dauke da cutar ko akasin haka a cikin dan kankanin lokaci sabanin yadda lamarin yake a baya inda a kan iya daukar kwanaki kafin samun sakamakon.

Da yake karin haske kan lamarin, gwamnan jihar ta Bavaria Markus Soeder baya ga wannan cigaba da aka samu, a share guda ya ce wadanda ba sa dauke da cutar kuma suke son a yi musu gwajin don radin kansu na da damar gabatar da kansu don yin gwajin kuma za su samu sakamakon kasa da mako guda.

Kasar Jamus dai na daga cikin kasashen Turai da su ka yi nasarar shawo kan wannan annoba tun a matakin farko wanda kawo yanzu mutanen da suka mutu ba su zarta dubu takwas da dari biyar ba.