1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olaf Scholz na ziyara aikin a Nijar

Binta Aliyu Zurmi
May 23, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz na ziyara a wasu kasashe na nahiyar Afirka a karon farko tun bayan kama aiki watanni shidda da suka gabata, batun matsalar tsaro da sauyin yanayi na da cikin dalilan wannan ziyara.

https://p.dw.com/p/4BkOp
Niamey, Niger | Kanzler Scholz besucht den Niger
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Olaf Scholz ya isa Jamhuriyar Nijar inda ya fara ganawa da sojojin Jamus da ke aikin horas da dakarun Nijar dabarun yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel.

Yanzu haka kuma shugaban na can yana ganawa da takwaransa na Nijar din Mohammed Bazoum a fadar mulki da ke birnin Yamai, inda tattaunawa tasu ta fi mayar da hankali kan siyasa da ma tsoro a yanklin na Sahel da ke fama da ayyukan 'yan ta'adda.

Wani batu har wa yau da shugabannin biyu za su mayar da hankali a kai shi ne batun bakin haure da ke kwarara zuwa nahiyar Turai ta barauniyar hanya.

Gabannin zuwansa Nijar dai, Scholz ya ziyarci kasar Senegal inda ya tattauna da shugaban kasar Macky Sall kan batutuwan da suka shafi tsaro a Afirka da kuma yakin da Rasha ke yi a kasar Ukraine.