1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na takatsantsan da manufofinta na Siriya

July 31, 2012

Ba a san tsawon lokacin da Assad zai iya jurewa ba, amma a bayan fage ana nazarin tsare tsare na bayan mulkin Assad.

https://p.dw.com/p/15hDW
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service A defaced poster of Syria's President Bashar al-Assad is seen near garbage containers in Aleppo July 24, 2012. The words on the poster read, "We coming, duck ass". Picture taken July 24, 2012. REUTERS/Shaam News Network/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Har yanzu shugaban Siriya Bashar Al-Assad na riƙe da akalar shugabancin ƙasar, sai dai ƙarfin ikonsa na raguwa. Masana sun yi nuni da cewa ba za a iya yin hasashen tsawon lokacin da shugaban zai iya jure wa ba. Amma ga ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yanzu an kai wani matsayi da babu maƙawa sai an samu sauyi a ƙasar ta Siriya.

A halin da ake ciki masana harkokin yau da kullum sun fara nuna fargaba ga halin da ƙasar ta Siriya ka iya faɗawa ciki bayan kawo ƙarshen mulkin gwamnatin Bashar al-Assad. Heiko Wimmen masanin ƙasar ta Siriya ne a gidauniyar nazarin tattalin arziki da manufofin siyasa dake birnin Berlin.

"Ba za iya yin hasashen lokacin da gwamnatin Assad za ta faɗi ba. Akwai hujjojin nuna fargabar cewa hakan ka iya ta da wata matsala. Wataƙila za a iya kifar da gwamnati, amma za a ci-gaba da samun magoya bayan gwamnati, 'yan gani kashe ni, da za su ci-gaba da yaƙi."

Siriya ka iya faɗa wa cikin mummunan hali

Masanin ya ƙara da cewa Siriya ka iya faɗawa cikin yaƙin basasa ko bayan Assad. Abu mafi muhimmanci shi ne tun yanzu a samar da wasu dubaru da tsare tsare tare da yin wani tanadi bayan gwamnatin Assad.

Heiko Wimmen
Heiko Wimmen-faɗuwar Assad ba za ta warware matsalolin baHoto: SWP

A cikin hira da wata jarida ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya nunar cewa ya zama wajibi a samar da wata alƙibla ko manufa da za ta dace da abubuwan dake faruwa a Siriya. Sai dai a nan ba a nufin Jamus za ta yi gaban kanta, domin kamar yadda Elmar Brok ɗan majalisar dokokin Turai ya nunar, damar da Jamus ke da ita ta yin katsalanda taƙaitacciya ce, dole ƙasar ta yi aiki da ƙungiyar tarayyar Turai. A saboda haka ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta gabata da wani daftarin shawarwari yadda ƙungiyar EU za ta tinkari rikicin na Siriya, musamman sabbin hanyoyin kawo ƙarshen tashe tashen hankula da ƙara yawa taimakon jin ƙai da aikin sake gina ƙasar bayan kawo ƙarshen gwamnatin Bashar al-Assad.

Tsarin farfado da tattalin arzikin Siriya bayan Assad

A cikin watan Agusta za a gabatar da sakamakon nazarin tsare tsaren da aka yi ga ƙasar ta Siriya. Lokaci da yadda za a aiwatar da waɗannan tsare tsare ga wata sabuwar ƙasar Siriya sun dogara kan abubuwa da dama. Misali tsawon lokacin da Assad zai ci-gaba da jurewa da ƙarfin zuciyar ƙungiyoyin adawa.

Wani batun kuma shi ne alƙiblar sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ta yadda al'ummominta za su samu damar faɗa a ji. Duk da cewa hanyar da nisa kafin wannan lokaci, amma masanin ƙasar Siriya Heiko Wimmen ya ce muhimmin abu shi ne tun yanzu a samu wani angizo a kan ayyukan raya ƙasa nan gaba.

A Free Syrian Army member aims his weapon after hearing shelling at Aleppo's district of al Sukkari July 29, 2012. REUTERS/Zohra Bensemra (SYRIA - Tags: POLITICS CONFLICT CIVIL UNREST MILITARY)
An damu da gumurzun da ake yi a AleppoHoto: Reuters

"A yi ƙoƙarin samun abokanen tattaunawa, domin tabbatar samun angizo a kan waɗannan mutane idan lokacin ya zo. Idan aka jira har wannan lokaci to za a rasa mutanen, kuma idan babu wani tsari kafin lokacin, to ba za a samu wani ba."

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya yi bayanin cewa ana da shirin tallafa wa al'ummar Siriya na tsawon lokaci a saboda haka tun yanzu an kafa harsashin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, inda ake aiki tare da aminan Siriya da haɗaɗɗiyar daular Larabawa. Jamus da ƙasar ta haɗiɗɗiyar daular Larabawa ke jagorantan aikin dake da nufin kirƙiro da wani dandalin shawarwari ga 'yan adawar Siriya dangane da tsarin tattalin arziki.

Mawallafa: Sabine Hartert-Mojdehi / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu