1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na shan suka kan kin taimaka wa Ukraine

Usman Shehu Usman RGB
February 14, 2022

Kasar Jamus ta yi watsi da batun sayar wa Ukraine da makamai bisa hujjar da gwamnatin ta bayar na cewa, kasar ba ta sayar da makamai a duk wata kasar da ake yaki.

https://p.dw.com/p/4703m
Symbolbild Rüstungsexporte aus Deutschland
Hoto: Bernd Weißbrod/dpa/picture alliance

Kasar Jamus ba ta sayar da makamai a kasar da ake yaki kamar yadda sanarwar gwamnatin ta tabbatar. To amma bincike ya gano cewa sau da dama Jamus ta karya irin wannan tsarin. Kawo yanzu kasar Rasha ta girke kimanin sojoji dubu dari a kan iyakar kasar da Ukraine, acewar jami’an leken asirin kasashen yamma. A bisa hakanne Ukraine da kasashen yamma ke cewa matakin na Rasha wata babbar barazana ce ga tsaron Ukraine. 

Kuma kasashe da yawa sun dauki matakin turawa Ukraine tallafin makamai, amma a bangaren kasar Jamus, kawo yanzu hular kwano kimanin 5000 ne kawai ta tura a matsayin gudumawa. Duk da cewa a hukumance kasar Ukraine ta mika takardar rokon Jamus ta tura mata makamai, amma shugaban gwamnati Olaf Scholz da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock , duk sun ki amincewa da hakan. Inda suka bayar da hujjar rigingimu da Ukraine ke fama da su. Pieter Wiezeman, wani masanin harkar kasuwancin makamai ya ce, siyasa ce kawai.

''Abubuwan da Jamus ke bayarwa ga kasar Masar za a iya raba su zuwa manyan sassa biyu. Daya shi ne samar da tsarin tsaro na sararin samaniya. Ba su da alaka da yakin Yemen, kamar yadda nake gani. Dayan kuma shi ne samar da jiragen ruwan yaki. Tabbas sojojin da kansu za su iya taka rawa a irin yakin da muka taba gani a kasar Yemen, a matsayin wani muhimmin bangare na hakan shi ne killace sojojin ruwa. Don haka kuna iya tunanin cewa wadannan jiragen ruwa a nan gaba za a iya amfani da su a cikin wani abu makamancin haka. Kuma wannan shi ne, tabbas babban abin damuwa ne“.

Ba wai kasar Masar ce kawai aka yi wa irin wannan gata daga kasar ba, amma tabbas akwai kasashe irin wannan, kuma yin hakan ya saba wa masu nuna fushinsu a cikin kafafen sadarwar zamani. "Tambayi Jamusawa game da jigilar makamai zuwa Saudiya, Masar, Turkiyya, in ji wani mai bin tashar DW daga Ukraine a shafinsa na Facebook ya ce, "Ana amfani da makaman Jamus a yake-yake da rikice-rikicen makamai a duk fadin duniya, shin hakan gaskiya ne?

Pieter Wiezeman cewa ya yi. ''Ina ganin ita kanta gwamnatin Jamus ta wata hanya ta yarda cewa wasu yanke shawara na ba da izinin fitar da makamai, a baya sun kasance kuskure ne, yayin da aka ba da wadannan makaman, an kara fitowa fili cewa, hadarin da ke tattare da shi na iya yin yawa kuma sun daina ba da su. Kuma lamarin ya kasance musamman a kasar Saudiya, inda aka yi wani gagarumin aiki na samar da jiragen ruwa na sintiri ga misali. Kuma duk da cewa wadannan jiragen sintiri ne kawai, gwamnatin Jamus ta yanke shawarar cewa ba abu ne mai kyau ba a ci gaba da sayar masu“.

Baya ga kasashen Gabas ta Tsakiya, masanan suka ce ai Jamus ta ba da makamai ga misali, Koriya ta Kudu wanda ba shakka har yanzu a cikin rashin zaman lafiya tare da Koriya ta Arewa. Kuma ba shakka, tana yin hakan ne da tunanin cewa tana taimaka wa Koriya ta Kudu don kare kanta daga yuwuwar cin zarafi daga Koriya ta Arewa. Don haka, me ya hana Jamus taimaka wa Ukraine da makamai?