1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na neman ƙarin haske game da binicken ƙungiyoyin waje a Masar

Charles Duguid PenfoldDecember 30, 2011

Jamus na shirin nuna wa jakadan Masar a Berlin rashin jin daɗinta game da kutsen 'yan sandan Masar a cibiyoyon kungiyoyon ƙetare guda 17 a Alƙahira.

https://p.dw.com/p/13bhE
Ma'aikatan kungiyoyi masu zaman kansu a MasarHoto: dapd

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bayyana cewa ta kira jakadan Masar a Berlin domin nuna ɓacin ranta da kuma nema ƙarin haske, game da binciken da jami'an tsaro suka gudanar a reshen gidauniyar Konrad Adenauer da ke babban birnin na Masar. A cewar kafofin watsa labaran wannan ƙasa, gidauniyar na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa guda 17 da 'yan sandan Masar suka kutsa cikinsu a ranar Alhamis domin binciken ƙwaƙwaf, bisa dalilai da suka danganta da bincike kan kafofin samun kuɗaɗe na ƙungiya masu zaman kansu da ke gudanar da ayyukansu a Masar.

Wani babban jami'in gwamnatin Amirka shi ma ya nuna damuwa game da matakin na Masar, tare da yin kira ga hukumomin Alƙahira da su daina shiga sharo ba shanu na harkokin ƙungiyoyin, waɗanda akasarinsu na ƙasar Amirka ne. Gwamnatin rikon ƙwarya ta mulkin sojan masar, ita ce ta yi alƙawarin yin nazarin hanyoyin da ƙungiyoyin da ke fafutukar kare demokaraɗiya da kuma 'yancin bil Adam suke samun kuɗaɗensu na shiga. Kana ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da duk wani shisshigi na ƙungiyoyin ƙasashen waje a harkokinta na cikin gida ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu