1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na duba yiwuwar sake kakaba dokar kulle

March 27, 2021

Ministan lafiya na Jamus Jens Spahn ya ce akwai yiwuwar kasar ta dauki tsattsaurar matakin dokar kulle saboda yadda annobar coronavirus ke kara yaduwa cikin sauri.

https://p.dw.com/p/3rHUJ
Berlin PK Gesundheitsminister Jens Spahn
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Hukumar da ke dakile yaduwar cutattuka ta kasar ta ce an sami sabbin masu dauke da cutar kimanin dubu 20 yayin da wasu dari da 5 da 7 suka mutu sanadiyar cutar a ranar Asabar, abin da ya sanya cibiyar Robert Koch ta yi gargadin cewa adadin ka iya haura hakan a nan gaba idan ba a dauki matakan da suka dace ba. Sai dai ministan ya ce za su tattauna don duba yiwuwar sanya dokar yayin bukukuwan Ista kamar yadda ta kasance a bara.