1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kara samun masu kamuwa da Corona a Jamus

December 11, 2020

Ministan kiwon lafiya a Jamus ya ce akwai bukatar sake tsaurara dokokin hana yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

https://p.dw.com/p/3maKj
Deutschland Coronavirus Impfzentrum Nürnberg Spahn Söder
Hoto: Daniel Karmann/dpa/picture alliance

Biyo bayan cigaba da samun masu kamuwa da cutar Corona da ake yi a kasar, ministan lafiya na Jamus Jens Spahn ya ce akwai tsananin bukatar sake tsaurara matakan hana yaduwar annobar ta COVID-19 a kasar ba tare da bata wani lokaci ba.

Ministan ya bayyana cewa dokokin kullen da yanzu haka ake ciki, sam basa biyan bukata duba da yadda alkalumman masu rasa rayukkansu da ma kamuwa da cutar ke kara hauhawa a duk rana ta lillahi.

Dama can shugabar gwamnatin kasar Angela Markel ta fara duba yiyyuwar hakan, ya yin da ta ziyarci zauren majalisar dokokin kasar a wannan makon.

Kawo yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar a rana guda ya kai mutane 29,875 inda kuma wasu 598 suka ce ga garinku nan duka a jranar Alhamis din da ta gabata.