1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na adawa da sabon zama da Namibiya

Daniel Pelz ZMA, MAB
September 2, 2022

Gwamnatin Jamus ta dage kan aiwatar da yarjejeniyar da ke cike da cece-kuce da ta amince da ita kan kisan kiyashin da aka yi a Namibiya a zamanin mulkin mallaka, duk da sarkakiyar da ake fuskanta wajen aiwatar da ita.

https://p.dw.com/p/4GMsW
Berlin Proteste gegen Kolonialverbrechen in Namibia
Hoto: Paul Zinken/dpa/picture alliance

An yi shiru game da sulhu tsakanin Jamus da Namibiya. Tun a watan Mayun shekara ta 2021 ne dai ake kan tattaunawa kan kisan kiyashin da aka yi a tsohuwar kasar Jamus ta Kudu maso Yammacin Afirka, amma har yanzu gwamnatocin kasashen biyu ba su rattaba hannu ba. Ko a lokacin 'yan adawar Namibiya da wasu daga zuriyar wadanda abin ya shafa sun bukaci a sake tattaunawa, sai dai bayan tsawon lokaci gwamnatin Jamus ta yi watsi da hakan.

A hirar da ya yi da tashar DW, 'yar majalisar wakilan Jamus daga jam'iyyar masu ra'ayin gurguzu  Sevim Dagdelen na da ra'ayin cewar gwamnati ba ta muradin biyan kudaden diyya.Ta ce: "Jamus na amfani da ikonta a kan Namibiya, wanda ya samo asali daga lokacin mulkin mallaka. Musamman bisa ga yawan zargi a cikin majalisar dokoki a Namibiya da bacin rai  a bangaren zuriyar mutanen da Jamus ta yi wa wannan ta'assa lokacin mulkin mallakar,  gwamnatin hadakar ta Jamus ta yi watsi da su da bukatunsu tare da Turawa Namibiya."

Deutschland Berlin Sevim Dagdelen
'Yar majalisar Jamus Sevim Dagdelen na kare muradun NamibiyaHoto: Britta Pedersen/zb/dpa/picture-alliance

Kazalika haka yawancin wakilan Herero da Nama ke gani. Sun bukaci ganawa da ministar harkokin wajen kasar ta Jamus Baerbock a watan Disamba domin neman sabuwar tattaunawa. Amma sun yi watsi da sanarwar hadin gwiwa saboda a cikinta Jamus ta yarda ne kawai bisa ka'ida, amma babu wani alhakin daukar nauyin game da kisan kiyashin a shari'ance.

Sun soki shirin sake gina yankunan da zai ci kimanin Euro biliyan 1.1 na taimakon sake ginawa cikin shekaru 30. "Wannan shi ne hadin kai na ci gaba.. Amma wannan yarjejeniya ba ta magance ainihin matsalar ba, musamman ma batun adalci da sulhu ba," in ji Sima Luipert mai fafutuka na kabilar Nama ya hirarsa da jaridar Der Spiegel a watan Yuni.