1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kwance tsaffin bama-baman da ba su fashe ba

August 21, 2018

Yayin da yanayin zafi na bazara ya karfafa a kasashen Turai wani abu da ya fito fili a Jamus shi ne kokarain kwance tsaffin bama-bamai a karkashin kasa tun na lokacin yakin duniya.

https://p.dw.com/p/33U1U
Deutschland Fliegerbombe in Köln-Deutz gefunden
Hoto: picture alliance/dpa/M. Becker

Har yanzu da akwai sauran lokaci kafin kawo karshen yanayin zafi a Turai. A wasu sassan Jamus ana samun matsanancin yanayin zafi. Bayan shafe makonni na fari akwai hadarin samun gobarar daji da kasadar fashewar bama-bamai da ke binne karkashin kasa tun yakin duniya na biyu, wadanda kuma ba su fashe ba.

Joachim Leippert jami'i mai kula da aikin binciken makamai a karkashin kasa a jihar Baden-Württemberg ya yi karin haske:

"Tsakanin bama-bamai 18 zuwa 25 ake samu kowace shekara a jihar Baden-Württemberg, kuma akwai akalla guda daya da yake tashi a shekara a Jamus."

Sai dai manyan bama-bamai masu nauyin kilogram 300 zuwa 1000 zai yi wuya su tashi saboda wutar daji sakamakon yadda suka nutse a karkashin kasa. Idan kuma ba a daji suke ba bama-baman tun na lokacin yakin dunyia na biyu suna kewayen da gidajen mutane suke ne, haka ka iya zama kasada.

Har yanzu ana cin karo da tsaffin bama-bamai lokacin aikin gine-gine
Har yanzu ana cin karo da tsaffin bama-bamai lokacin aikin gine-gineHoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

Akwai dai dubban bama-baman da suke binne karkashin kasa a sassan Jamus kamar yadda kwararru suka tabbatar. Galibi a manyan birane da wuraren da baya suka kasance na harkokin sojoji. Amma har da kananan garuruwa gami da daji ana samun bama-baman a wuraren da dakarun kawance na yakin duniya na biyu suka kai samame.

Joachim Leippert jami'in ya ce 'yan sanda na daukar matakan da suka dace lokacin kwashe mutane a wuraren da aka gano irin wadannan bama-baman da ba su fashe ba.

"'Yan sanda suna aikin kwashe mutane a yankin da aka samu bama-baman a karkashin kasa. Girman bam yake nuna yawan iyaka da za a kwashe mutane."

A 2017 an kwashe mutane dubu 50 daga gidajensu a Hannover lokacin kwance wani bam
A 2017 an kwashe mutane dubu 50 daga gidajensu a Hannover lokacin kwance wani bamHoto: picture-alliance/dpa/P. Steffen

Sannan masanin ya kara da cewa kimanin ton 87,000 na bama-bamai aka jefa a jihar ta Baden-Württemberg lokacin yakin duniya na biyu. A gaba daya kimanin ton miliyan biyu aka dagargaza wa Jamus lokacin yakin duniya na biyu. Joachim Leippert ya ce ana samun hadin kai lokacin da yanayi ya taso na samun tsaffin bama-bamai.

"Har yanzu mutane suna mamaki, idan 'yan sanda suka ba da gargadi lamarin ya fi zama cikin hanzari."

Sannan ya yi bayanin yadda suke raba bam da aka samu wajen cire dan bakin kafin dauka daga wurin da aka samu sannan jami'in Joachim Leippert mai kula da aikin na binciken makamai a karkashin kasa a jihar Baden-Württemberg ya tabbatar matakan suna kan tsari.

"Haka aikin ya kasance babu hadari, amma muna yin abubuwa da dama kan hanya, sai dai wani lokaci abubuwa kan dagule."

Wani lokaci ana gano bama-baman inda ake tonon gine-gine. Lamarin da ya saka duk lokacin da za a yi aikin gine-gine ake amfanin da fasaha na zamani domin gano ko akwai bama-baman na lokacin yakin duniya na biyu.