1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta ziyarci Indiya

Abdoulaye Mamane Amadou
November 1, 2019

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa Jamus da Indiya na fatan karfafa alakar da ke tsakaninsu ta fuskancin fasahohin zamani da yaki da sauyin yanayi da kuma samar da makamashin da ake sabuntawa.

https://p.dw.com/p/3SLLm
Neu Dehli Merkel bei Modi
Hoto: AFP/P. Singh

Merkel ta bayyana hakan ne bayan kammala tattaunawa tsakanin gwamnatocin Jamus da Indiya karo na biyar a birnin New Delhi. A yayin ziyarar ta kwanaki uku da Merkel ke yi a Indiyan za su tattauna kan batun bunkasa dankgantakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangaren Firaministan Indiyan Narendra Modi ya yi bayani kan fannoni daban-daban da kasashen biyu suka yi aiki tare kuma da cimma nasara musamman batun kimiyya. Yayin ganawar shugabannin biyu dai, sun cimma yarjejeniya kan batutuwa har 22 da suke son yin aiki tare.