1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Heiko Maas zai fara ziyara a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 2, 2018

Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus Heiko Maas ya nunar da cewa akwai danganta mai karfi tsakanin Jamus da kasashen Afirka da dama.

https://p.dw.com/p/2x49d
Kanada - G7 Toronto | Bundesaußenminister Heiko Maas gibt ein Pressestatement
Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus Heiko MaasHoto: Imago/photothek/T. Trutschel

Maas ya bayyana cewa dangantakar da ke tsakanin kasarsa da Afirkan ce ma ta sanya Jamus din ke da kyakkyawar alaka da kungiyar Tarayyar Afirka AU. Kalaman na Maas dai na zuwa ne gabanin wata ziyarar aiki da zai fara a kasashen Habasha da Tanzaniya, inda ya nunar da cewa yana farin cikin wannan ziyara da zai kai a karo na farko a matsayinsa na ministan harkokin kasashen ketaren Jamus. Ya kara da cewa suna da alaka mai karfi ta fuskacin siyasa da tsaro da wasu kasashen Afirka da dama. Maas ya nunar da cewa a Habasha zai tattauna da kungiyoyin farar hula da ma gwamnati domin tabbatar da ganin an aiwatar da sababbin sauye-sauyen da sabon Firaministan kasar ke son aiwatar wa, da nufin yin sulhu tsakanin kabilun kasar da ke rikici da juna, yayin da a Tanzaniya ya ce zai ziyarci wata makaranta da ake koyon harshen Jamusanci.