1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haraji a kan masallatai a Jamus

Abdourahamane Hassane
December 27, 2018

Gwamnatin hadaka ta Jamus ta ce tana tunanin saka kudaden haraji a kan masallatai kamar yadda ake biyan haraji na Cocina.

https://p.dw.com/p/3Agaw
Sehitlik Moschee in Berlin
Hoto: Getty Images/C. Koall

Gwamnatin Jamus ita ce ke cire harajin wa mabiya al 'ummar Kirista, amma kuma daga baya kudaden da ta zabtaren na harajin  ta zubasu ga hukumomin kula da Cocina domin gudanar da aikace-aikacen na Cocin. Thorsten Frei, wani na kusa da shugabar gwamnatin Angela Merkel  ya ce girka haraji zai kara ba da dama wajen habakar Musulumcin a Jamus, sakamakon tallafin da hukumomin addinin Musuluncin za su rika samu daga gwamnatin Jamus don gudanar da aika-aikace na masallatai.