1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Dan bindiga ya bude wuta kan jama'a

Binta Aliyu Zurmi MNA
January 24, 2020

An kai harin bindiga a garin Rot Am See da ke jihar Baden-Würtemberg da ke kudancin kasar Jamus inda aka samu asarar rayukan mutum shida.

https://p.dw.com/p/3WmTN
'Yan sanda a wurin da aka yi harbe-harben da ke a garin Rot am See
'Yan sanda a wurin da aka yi harbe-harben da ke a garin Rot am SeeHoto: picture-alliance/dpa/S. Gollnow

Harin bindigar da 'yan sanda suka danganta shi da na kashin kai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shidda tare da jikata wasu da dama. Jami'an 'yan sanda a garin Rot Am See da ke jihar Baden-Würtemberg na kudancin Jamus suka fidda wannan sanarwar a shafinsu na Twitter.

Har wayau sanarwar ta kara da cewar tuni aka damke mutum guda da ake zargi da kai harin, sai dai ba a kai ga sanin ko shi kadai ne ya kai harin ba da ma dalilansa na aikata wannan ta'asa.