1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Kenya sun shirya a kan daukar baki aiki

September 13, 2024

Jamus ta amince da Kenya a kan batun da ya shafi daukar kwararrun 'yan kasar da ke gabashin Afirka aiki, daidai lokacin da Jamus ke fadi tashin cike gibin da ke gabanta na masu ritaya.

https://p.dw.com/p/4kcGY
William Ruto na Kenya da Olaf Scholz na Jamus
William Ruto na Kenya da Olaf Scholz na Jamus Hoto: Political-Moments/IMAGO

Kasashen Jamus da Kenya, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta ba da damar daukar 'yan kasar Kenya masu kwarewa a fannin sana'o'in hannu aiki.

An cimma yarjejeniyar ne dai a birnin Berlin yayin wata ziyarar da Shugaba William Ruto ya kawo nan Jamus a yau Juma'a.

Yarjejeniyar ta kuma zo ne yayin da Jamus a gefe ke rufe kokfofinta ga bakin 'yan kasashen ketare masu share wuri suna zama cikin kasar ba tare da samun izini ba.

Haka nan ma yarjejeniyar ta hada da batun mayar da 'yan kasar Kenya da ba a amince da zamansu ba a Jamus zuwa gida.

Jamus dai na fama da karancin ma'aikata musamman a kamfanonin kasar saboda yawan tsofaffi wadanda ke ajiye aiki, abin da ke sanya ta bukatar majiya karfi da kuma ke da kwarewa daga wajen kasar.