1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabunta dangantakar Jamus da Birtaniya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 2, 2021

Birtaniya da Jamus na son sabunta dangantakar da ke tsakaninsu ta hanyar amafani da sabuwar yarjejeniya da kuma tuntuba tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3vxkz
UK Besuch der deutschen Bundeskanzlerin Angela Merkel
Firaministan Birtaniya Boris Johnson da shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: David Rose/Daily Telegraph/empics/picture alliance

Firaminstan Birtaniya Boris Johnson da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ne suka sanar da wannan kudirin, jim kadan bayan ganawar da suka yi a kusa da birnin London na Birtaniyan. Gwamnatocin kasashen biyu da wasu daga cikin ministocinsu za su rika tuntuba da kuma samun bayanai tsakaninsu sau guda a shekara, matakin da zai ba su damar tsara kawance ko kuma hadin kai a tsakaninsu. Merkel ta yi wa Johnson alkawarin cewa, ba da jimawa ba Jamus din za ta rage tsauraran matakan kariya da ta sanya kan kasarsa sakamkon nau'in annobar coronavirus na Delta da ake fama da ita a Birtaniyan.