1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus ta kama mutun 1500 a wata mayanka da ke Jamus

June 23, 2020

Annobar corona ta barke a wata mayanka da ke jihar North Rhine-Westphalia a tarayyar Jamus inda mutun 1500 suka kamu a wata mayanka da ake kira Tönnies.

https://p.dw.com/p/3eEPZ
Deutschland | Coronavirus | Lockdown Gütersloh | Rheda-Wiedenbrück | Tönnies
Mayakar nama ta Tönnies inda cutar corona ta bullaHoto: picture-alliance/dpa/G. Kirchner

Wannan dai shi ne karon farko a tarayyar Jamus aka dauki wannan mataki mai tsaurin gaske a ilahirin wata gunduma don yaki da annobar coronavirus, kamar yadda Firimiyan jihar North Rhine-Westphalia da gundumar ta Gütersloh ke cikinta, Armin Laschet ya yi bayani. Matakin zai ci gaba har zuwa ranar 30 ga watan nan na Yuni, saboda haka firimiyan ya yi kira ga al'ummar yanki su kusan dubu 400 da kada su bar yanki, ko da yake kulle ba ya nufin an haramta yin tafiye-tafiye. 

Deutschland | Coronavirus | Lockdown Gütersloh | Ministerpräsident Laschet
Firimiyan jihar North Rhine-WestphaliaHoto: picture-alliance/dpa/F. Gambarini
Gütersloh Ausbruch bei Tönnies | Proteste
Masu zanga-zanga kan annoba a TönniesHoto: Imago Images/teamwork/A. Duwentäster

Yanzu haka dai an girke 'yan sanda da ma'aikatan jinya da na kwana-kwana a garin Rheda-Wiedenbrück da ke a gudunmar don dakile yaduwar cutar, bayan da sama da ma'aikata 1500 daukacinsu baki 'yan ci-rani daga kasashen gabashin Turai masu aiki a mayanka ta Tönnies suka harbu da cutar ta Covid-19.                                        Mazauna garin sun boye                  Daukacin mazauna garin sun san hali da ake ciki amma sun ki cewa uffan. Amma ba haka yake ba ga wata mai fafatuka, Inge Bultschnieder, wadda tun a wasu shekaru take korafi game da mummunan yanayi na aiki da wurin zama ga ma'aikatan. A wani gida da wasu ma'aikata 13 'yan asalin kasar Romaniya ba su dade da tashi ba an ga yadda muni yanayin zamansu yake, kamar yadda mai fafatukar ta nunar, inda ta ce: "Kwani 10 zuwa 14 da suka tashi daga wannan gida, da yanzu haka yake wari. A watan Disamban shekarar 2018 mun yi zanga-zanga a gaban gidan don nunawa duniya halin da ake ciki." Anderj Ionescu da ba shi ne sunansa na asali ba, dan kasar Romaniya ne da ya yi aiki a mayankar ta Tönnise tsawon shekaru biyu, amma ya bari aikin saboda rashin biyansa kudin abataya ko overtime da Ingilishi, yana mai cewa "Lokacin aikin shi ne mafi muni a wannan kamfani. Muna fara aiki da karfe daya na rana mu tashi da karfe daya na dare, wato sa'o'i 12 a rana." Zanga-zanga bayan annoba    Bayan samun barkewar cutar a kamfanin na Tönnies hukumomi da ma al'umma na fargaba cutar za ta yadu a tsakanin mazauna garin da ma kewaye inda wasu daga cikinsu sun shedawa DW da cewa sun damu "Na damu ina kuma jin tamkar mun rasa gano bakin zaren matsalar. Ba mu san abin da zai faru nan gaba ba." Tuni dai an rufe mayankar ta Tönnies. Annobar ta kuma bankado matsalolin da mai fafatuka Inge Bultschnieder ta yi ta kokarin janyo hankalin humumomi a kai tsawon shekaru. Sai yanzu mahukunta suka mayar da hankali sosai kan akubar da ma'aikata ke ciki a mayankar.

Inge Bultschnieder
Inge Bultschnieder 'yar fafutikaHoto: DW/M. Soric