1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Jamus ta samu mafita kan batun Diesel

Salissou Boukari
October 2, 2018

Gwamnatin Jamus ta cimma matsaya kan makomar miliyoyin mutane da ke da tsaffin motoci masu amfani da man Diesel, wanda kuma hayakin da suke fitarwa ya fice kima.

https://p.dw.com/p/35qh4
Deutschland Mercedes beim TÜV in Hildesheim
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Stratenschulte

An dai gudanar da wani zama ne a ran Litinin har cikin dare a birnin Berlin a tsakanin manyan jagororin jam'iyyar SPD da ke cikin kawancen da ke mulki, da kuma jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da abokiyar kawancenta ta kullum ta CSU, inda suka ce sun samu mafita na magance yawaitar gurbatacen hayaki a manyan biranen kasar.

Sai dai ya zuwa ranar wannan Talatan ce dai ake sa ran gwamnatin za ta sanar da matakai, wanda tuni ake ganin babban nauyin zai rataya ne kan kamfanin kera motocin da a baya ya yi coge kan sanar da gaskiyar lamari na hayakin da motocin da ya ke kerawa masu amfani da man diesel suke fitarwa.