1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar Lafiya a Jamus ta sallami wasu mutane da aka killace

Zulaiha Abubakar
February 16, 2020

Akalla mutane 100 yan asalin kasar Jamus ma'aikatar Lafiya ta sallama daga cibiyar da suke killace bayan kwaso su daga Wuhan ta kasar Chaina yankin da annobar cutar Coronavirus ta yi kakagida.

https://p.dw.com/p/3Xrbj
Berlin Flughafen Tegel Evakuierte aus Wuhan
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Sakataren Lafiya na Jamus Thomas Gebhart, ya shaidawa manema labarai cewar gabanin sallamar mutanen sai da jami'an lafiya a Jamus suka tabbatar basa dauke da kwayar cutar wacce ta hallaka sama da mutane 1,600 a Chaina. Makwanni biyu dai matafiyan suka kwashe killace a wani sansanin sojin Jamus da ke dab da filin jiragen sama na birnin Frankfurt.

Jamus dai ta kasance kasa guda cikin kasashen Turai da aka samu akalla mutane 16 sun kamu da cutar duk kuwa da cewar har ya zuwa yanzu wadanda suka kamun basu shiga mawuyacin hali ba kuma babu asarar rai.