1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamiyyun adawan Jamus sun goyi bayan tallafin Girka

February 27, 2012

Girka ta kama hanyar samun tallafin dala milliyan dubu 130 wanda aka alkawarta mata kasancewar Majalisar Dokokin Jamus na Bundestag ta bada goyon bayanta

https://p.dw.com/p/14B2m
German Chancellor Angela Merkel (C) and other parliamentary deputies vote on a Greek bailout package in the Bundestag, the lower house of parliament, in Berlin , February 27, 2012. Germany's parliament was almost certain to endorse a second Greek bailout on Monday but Chancellor Angela Merkel was torn between domestic pressure to stop throwing good money after bad and global calls to boost Europe's crisis defences. REUTERS/Thomas Peter (GERMANY - Tags: POLITICS BUSINESS TPX IMAGES OF THE DAY)
Mahawaran amincewa da tallafin Girka a majalisar ta BundestagHoto: Reuters

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ya kamata a dauki shirin tallafin da za'a baiwa Girka da mahimmancin. A wani jawabi da ta gabatar a majalisar dokokin Bundestag a wannan litinin ta kuma yi la'akari da irin hatsarin da bayar da wannan tallafin ke tattare da shi. To sai dai Merkel ta bayyana cewa babu wanda zai iya bada tabbacin cimma nasara dari bisa dari bayan an aiwatar da wannan shiri, to amma abu mai mahimmanci shine za'a tabbatar da dorewar manufofin Turai da ma zamanta tamkar tsintsiya madaurin ki daya, idan har aka tabbatar da darajar takardar kudin ta euro. Shugabar gwamnatin ta kuma yi kira ga Girka da ta zage dantse wajen ganin ta aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata a fuskar gwamnatinta da tattalin arzikinta.

Majalisar ta Bundestag ta nuna goyon bayanta bayan da ta kada kuri'a, to sai dai har yanzu ba'a tantance yawan kudin da Jamus zata fitar ba. Ko da yake ana sa ran nan ba da dadewa ba za'a yanke shawarar kan yawan kudin, kasancewar jamiyyun adawa na SPD da Grüner sun bada goyon bayansu ga shirin tallafin.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita:           Usman Shehu Usman