1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyu ba su ji dadin shigar AfD majalisa ba

Ahmed Salisu
September 24, 2017

Jam'iyyun Jamus sun nuna rashin jin dadinsu kan shiga majalisa da jam'iyyar nan ta AfD mai kyamar baki ta yi. Jam'iyyar dai ta samu kashi sama da 13 cikin 100 a hasashen sakamako na farko da aka fidda.

https://p.dw.com/p/2kcr3
Bundestagswahl 2017 | CDU Anhänger
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Carstensen

Jam'iyyun Jamus suka ce abin takaici ne irin nasarar da AfD ta samu na shiga majalisa wanda hasashen da aka yi ke nuna cewar yawan kujerunta a majalisa za su iya kaiwa 88. SPD da ke adawa ta ce wannan matsayi da AfD din da ke kyamar baki ta kai abin tashin hankali ne. Ita ma dai jam'iyyar Merkel ta CDU ta ce ba ta ji dadin wannan labari ba amma ta ce za ta yi bakin kokarinta wajen ganin ta kwace magoya bayan da jam'iyyar ke da su a fadin kasar. Tuni dai jam'iyyar ta ce in majalisa ta fara zama za ta bukaci a kafa wani kwamiti da zai binciki Merkel kan shirinta na karbar baki wanda AfD din ke adawa da shi.