Jam'iyyu a Mali sun katse tattaunawa a kan zabe
July 23, 2024'Yan siyasar kasar Mali da gwamnatin mulkin soja ke tsare da su a gidan yari sun hada da Mohamed Ali Bathily da ke zma ministan shari'a a karkashin mulkin Ibrahim Boubacar Keita da Yaya Sangaré da ke kula da ma'aikatar sadarwa a tsohuwar gwamnatin farar hula da kuma tsohon ministan ilimi mai zurfi Moustapha Cissé na jam'iyyar ADEMA. Hasali dai, masu shrhi an fnnin siyasa sun yin intifakin cewar dukkanin 'yan siyasa na da rawa da za su iya takawa wajen ciyar da jam'iyyarsu ko ma tsarin zaben Mali gaba idan aka yi amfani da shawarwarinsu.
Sai dai neman mayar da wasu kusoshin tsohuwar gwamntin Ibrahim Boubacar Keita saniyar ware ya sa hadakar jam'iyyu da kungiyoyin farar hula na Mali rattaba hannu a ranar 31 ga Maris kan sanarwar kaura ce ma duk wani zama da bangaren gwamnatin mulkin mulkin soja kan shirin mayar da Mali kan tafarkin mulkin farar hula ko dimukuradiyya. Dama dai, hukumar zaben Mali ba ta tsayar da jadawalin zaben shugban kasa da 'yan majalisa ba, amma tana kokarin jawo 'yan siyasa a jika don cimma matsaya kan alkiblar da za dosa game da zabe.
Karin bayani: Sojojin Mali sun haramta al'amuran siyasa a fadin kasar
Yehia Adama Maiga da ke shugabantar jam'iyyar Malidenwn Hakilina ya goyi bayan matakin da takwarorinsa suka dauka na kaurace ma zaman, yan mai cewar tsarin zai shafi yunkurin da ake na mayar da Mali tsintsiya madaurinki daya:
"Saboda idan kuna son ku girka wani tsari, wannan yana nufin cewar dole ne a dama da kowa. Amma idan muka mayar da mutum saniyar ware ta hanyar kama shi, a bayyane yake cewa wannan tsarin ba zai iya ba da sakamakon da ake tsammani ba. Dole ne a sake su don su shiga a dama da su a harkokinn siyasar kasarsu."
A daidai lokacin da akasarin jam'iyyun siyasar kasar ta Mali ke kin ba wa hukumomin mulkin soja kai domin boiri ya hau, hukumar AIGE (Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta) ta nuna a nata bangaren cewar ta himmatu wajen na shirya zabuka daban-daban. Sai dai ta kara da cewa tana jiran umurni daga hukumomin Bamako.
Amma Salia Kariba Traoré ta COCEM wata gamayyar kungiyoyi da ke sa ido kan zabe a Mali ya ce akwai bukatar aiwatar da gyare-gyare masu mahimmanci kafin a shirya zabuka masu zuwa.
"Wadannan gyare-gyaren za su kasance a kan dokar zabe domin bai wa ‘yan kasar Mali da ke kasashen waje damar tsayawa takara a zaben ‘yan majalisar dokoki. Kuma kamar yadda ka sani, sabon kundin tsarin mulki ya tanadi kafa majalisar dattawa. Dole ne a aiwatar da wadannan tanade-tanade kafin a je zabe, sannan akwai tsawaita zagaye na biyu a lokacin zaben shugaban kasa. Akwai sabbin yankuna da aka kafa, wadana dole ne a yi la'akari da su wajen gudanar da sauye-sauye."
Baya ga sauya tsarin zaben da har yanzu ake ci gaba da yi, ba a warware matsalar yawan kudi da hanyoyin da za a samo su ba. Sai dai abin da ya fito fili shi ne, babu tanadin kudaden da ake bukata don gudanar da zaben shugaban kasa da aka yi a cikin kasafin kudin shekarar 2024 ba. Kazalika, hukumar zabe mai zaman kanta ba ta kafa rassanta a yankunan kasar ta Mali ba. Dangane da rajistar masu kada kuri'a kuwa, har yanzu ba a kayyade ranar farawa ba.