1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Merkel ta sha da kyar a zaben Hessen

Salissou Boukari
October 28, 2018

Sakamakon farko na zaben da ya gudana a jihar Hessen da ke yammacin Jamus ya nunar cewa jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ce ke kan gaba a kuri'un da aka kada idan ta samu kashi 28 cikin 100.

https://p.dw.com/p/37HbF
Deutschland, Fulda: Der hessische Ministerpräsident Volker Bouffier Bundeskanzlerin Angela Merkel nehmen an der letzten Wahlkampagne vor den bevorstehenden Landtagswahlen teil
Hoto: REUTERS

Duk da cewar CDU ta samu nasara a zaben wannan sakamako ya nunar da cewa ta samu gagarumin koma baya idan aka kwatanta da zaben shekara ta 2013. Ita ma dai jam'iyyar SPD da ke cikin kawancen da ke mulki a nan Jamus ta samu nasara a zaben da kashi 20 cikin 100 sabanin na 2013 inda ta samu kashi 30 cikin 100 a wannan jiha ta Hessen, abun da ke nuni da cewa dukanninsu sun samu koma baya ida aka yi la'akari da abin da jam'iyyun suka samu a zaben da ya gudana shekaru 5 din da suka gabata.

Ita kuwa jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli nasara ta samu a nata bangare idan aka yi la'akari da irin abin da ta samu a zaben da ya gabata na 2013 inda ta samu kashi 8 cikin 100 yayin da a wannan karon ta samu kusan kashi 20. Jam'iyyar masu tsatsauran ra'ayi na kyamar baki ta AfD kuwa ta samu kashi 13 daga cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.