1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi ke da rinjaye a EU

June 10, 2024

Jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi a kungiyar Tarayyar Turai na ci gaba da samun rinjaye, duk da nasarar da masu tsattsauran ra'ayi suka samu a zaben majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/4gr2o
Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar ta EU, Ursula von der Leyen
Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar ta EU, Ursula von der LeyenHoto: Geert Vanden Wijngaert/AP/dpa/picture alliance

Duk da gagarumin nasarar da jam'iyyar masu tsattsaurar ra'ayi suka samu a kasashen Faransa da Jamus da kuma Austria a zaben majalisar dokokin kungiyar Tarayyar Turai, har yanzu jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi ne ke kan gaba a majalisar dokokin ta EU. Sakamakon zabukan dai na ci gaba da nuni da cewa, jam'iyyar al'umma ta European People's Party (EPP), za ta tsaya a matsayinta na mafi rinjaye a majalisar.

Karin bayani: Kawancen jam'iyyun CDU/CSU na kan gaba a zaben EU da aka kammala

Bisa dukannin alamu, shugabar hukumar gudanarwar kungiyar ta EU, Ursula von der Leyen na kan hanyar ci gaba da jagorancin kungiyar har zuwa shekarar 2029.

Karin bayani: Ursula von der Leyen na da muradin sake neman shugabancin EU

A makwanni masu zuwa ne, von der Leyen za ta nemi samun goyon bayan mafi yawan 'yan majalisar, domin amince mata a matsayin shugaba a karo na biyu.