1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu kyamar baki na kara karbuwa a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
September 21, 2018

Farin jini na Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na kara yin kasa, yayin da jam'iyyar masu kyamar baki Alternative for Germany (AfD) ke kara samun karbuwa a tsakanin masu zabe a Jamus, a kuri'ar jin ra'ayin jama'a.

https://p.dw.com/p/35Jox
Deutschland Logo der AfD
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Gateau

A kuri'ar jin ra'ayin jama'a da kafar yada labarai ta Jamus ARD ta fitar bayan tattara bayanai tsakanin ranar 17 ga watan Satimba zuwa 19 ga watan, ya nunar da cewa jam'iyyar CDU da babbar abokiyar jam'iyyar wato CSU da jam'iyyar SPD za su iya samun kashi 45 cikin dari ne a zabe.

Kawancen na CDU/CSU masu ra'ayin mazan jiyan na da kashi 28 cikin dari ne, wannan kiyasi ya sanya jam'iyyun sun sami kaso mafi kankanta tun da aka fara irin wannan kuri'ar jin ra'ayi a 1997. Ita kuwa jam'iyyar ta AfD na da 18 cikin dari sabanin 12.6 cikin dari da take da shi a Satimbar shekarar bara.