1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jam'iyyar hamayya na gaba a zaben Zambiya

August 14, 2021

Sakamakon farko na zaben kasar Zambiya, na nunin cewa kuri'un da jam'iyyar hamayya na gaba da wadanda jam'iyya mai ci ta samu kawo yanzu, a cewar hukumomi.

https://p.dw.com/p/3yyvl
Sambia Präsidentschaftswahlen Wahlen
Hoto: Patrick Mainhardt/AFP/Getty Images

Sakamakon na nunin cewa babban dan hamayya a Zambiya, Hakainde Hichilema, na gaba da abin da shugaba mai ci Edgar Lungu ya samu, kamar yadda hukumar zabe ta nunar a yau.

Mr. Hichilema na da kuri'u dubu  171 da 604 yayin da Shugaba Lungun ke da dubu 110 da 178 cikin manyan mazabu 15 da shugaban ke da karfi a cikin su.

Jimillar kuri'u dubu 296 da 210 ne dai aka kada a wadannan mazabu, a cewar wani jami'in zaben da ya zanta da kamfanin dillancin labaru na Reuters.

Ana dai ganin samun sakamakon zaben na Zambiya na iya kaiwa yammacin ranar Lahadi, zaben kuma da jam'iyya mai mulki ke kurarin tana kan hanyar lashe shi.