1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar adawa ta ci zabe a Spain

July 24, 2023

'Yan adawa a Spain na murnar samun nasara a zaben kasa da aka kammala a karshen mako. Jam'iyyar Socialist ta Firaminista Pedro Sanchez ce ta zo ta biyu a zaben.

https://p.dw.com/p/4UISu
Alberto Nunez Feijoo
Hoto: Manu Fernandez/AP/picture alliance

Jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin rikau a Spain ta yi nasara, daidai lokacin da aka kammala kirga kuri'un da aka kada a zaben kasar da aka yi a jiya Lahadi.

Sai dai jam'iyyar ba ta kai ga samun kujerun da ake bukata a majalisar kasar ba, don haka dai ba ta samu rinjayen kafa gwamnati ba.

Kafin dai jam'iyya ta tabbata mai nasara, ana bukatar ta samu akalla kujeru 176 daga cikin 350 da ake da su a majalisar dokokin.

Jam'iyyar Socialist Workers' ta Firaminista Pedro Sanchez dai ta zo ta biyu ne a zaben da kujeru 122 da ke matsayin kashi 32% ke nan na sakamakon zaben.

Akwai yiwuwar a kwashe wasu makonni kafin a kai ga tabbatar da cikakken sakamakon zaben.