1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyar 'yan mazan jiya ta lashe zabe a Spain

November 21, 2011

Illolin kariyar tattalin arziki sun jawo babban koma baya ga jam'iyar gurguzu a Spain wadda ta sha mummunan kaye a zabe.

https://p.dw.com/p/13EM1
Mariano RajoyHoto: picture-alliance/dpa

Jam'iyar masu ra'ayin rikau a kasar Spain,ta lashe zaben 'yan majalisa da aka shirya tare da gagaramin rinjaye.

Daga jimlar kuri'un da aka kada,jam'iyar gurguzu mai rike da ragamar mulki ta samu kashi 29 cikin dari.

Wannan mummunan kayi na da nasaba da yadda Firaminista Zapatero, ya kasa shawo kan matsalar tattalin arziki da Spain ke fama da shi.

Tsofan ministan cikin gida Mariano Rajoy, shine za a rantsar a matsayin saban Firaminista.

A yayin da ya ke bayani jim kadan bayan bayyana sakamakon, saban Firaministan na cewa: wajibi ne su yi murnar nasara da suka samu, amma fa sai al´umar kasa gaba daya ta basu hadin kai ,sannan su cimma burin da suka sa gaba.

Wannan buri shine farfado da tattalin arzikin kasa, da kuma biyan bashin da ya kai Spain iya wuya.A yanzu haka, yawan marassa aikin yi a kasar Spain,ya kai addadin kashi kusan 22 cikin dari, wanda shine addadi mafi yawa a tsakanin kasashen EU.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Abdullahi Tanko Bala