1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyar RPT a Togo ta lashe zaɓen ´yan majalisar dokoki

October 18, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8F

Jam´iyar shugaba Faure Gnassingbe wadda ta shafe kimanin shekaru 40 tana jan ragamar mulki a Togo ta lashe zaben ´yan majalisar dokoki da aka gudanar kasar a ranar lahadi da ta wuce. Sakamakon wucin gadi da aka bayar yayi nuni da cewa jam´iyar RPT ta samu kujeru 49 daga cikin 81 na majalisar dokoki dake birnin Lome. Ita kuwa jam´iyar adawa ta UFC ta samu kujeru 21. Jam ´iyar ta UFC tana karkashin jagorancin Gilchrist Olympio ne dan tsohon shugaban Togo da aka yiwa kisan gilla a shekarar 1963 wato Sylvanus Olympio. ´Yan adawa sun zargin gwamnati da sayen kuri´u a arewacin kasar. To amma masu sa ido na KTA da na KTT sun bayyana zaben da cewa an kamanta gaskiya da adalci a cikin sa.