Jami'an tsaron Spain sun kama 'yan China
December 14, 2016Rundunar 'yan sandan kasar ta Spain ce dai ta sanar da wannan labari, inda ta ce wannan shi ne babban bincike na hadin gwiwa da ta aiwatar tare da 'yan sandan kasar China domin binciko yadda wadannan 'yan danfara ke tafiyar da nasu miyagun ayyukan.
Wannan kamu dai ya shafi 'yan asalin kasar ta China da ke aiki a gidajen wayar sadarwa da ake kira "Call centers" da ke wani kasaitaccen wuri na tsakiyar birnin Madrid, da birnin Barcelona da ke Arewa maso gabshin kasar, da kuma birnin Alikante da ke Kudu masu gabashi, inda ake zarginsu da laifin danfarar dubban 'yan kasar ta su kudaden da suka kai Euro miliyan 16.
Da yake magana yayin wani taron manema labarai, komishinan 'yan sandan birnin Madrid Eloy Quiros, ya ce hukumomin kasar China ne dai suka tuntubesu cewa wasu na danfarar 'yan kasar ta China da dama ta hanyar kiran waya. Babban jami'in 'yan sandan ya ce fiye da 'yan sanda 600 ne suka aiwatar da wannan bincike da ya kai ga gano cewa 'yan danfarar na da rassa a wasu kasashe da dama na duniya.