1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jami'an tsaro sun sake afka wa 'yan Sudan

January 6, 2022

Masu zanga-zanga a Sudan sun sake arangama da jami'an tsaro daidai lokacin da masu boren suka lashi takobin danganwa da fadar shugaban kasa a Khartoum

https://p.dw.com/p/45EaM
Sudan Khartum | Protest gegen Militärjunta, Ausschreitungen
Hoto: AFP/Getty Images

Jami'an tsaro a Sudan, sun afka wa dubban masu zanga-zangar da ke neman a dawo da kasar bisa turbar dimukuradiyya a wannan Alhamis

Rahotanni na cewa jami'an na tsaro sun kashe akalla mutum guda, bayan harbi da suka yi masa a ka.

Da farko dai hukumomin na Sudan sun datse hanyoyin sadarwa ciki har da na Intanet a kokarinsu na rage hanzarin shirye-shiryen da masu zanga-zangar adawa da gwamnatin.

Haka nan ma hukumomin sun toshe wasu manyan gadoji da ke Khartoum babban birnin kasar, da ma wasu da ke a biranen Bahri da Omdurman.

Sai dai masu zangar-zangar sun lashi takobin isa fadar shugaban kasa da ke a birnin Khartoum, a ci gaba da matsa wa mahukuntan sojin lamba.