Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Siriya sun ziyarci Haula inda aka kashe mutane 92
May 26, 2012Harin da aka kai daga tsakar ranar Juma'a zuwa asubahin yau asabar a garin Houla, ya yi sanadiyar rasuwar fararen hula 60 da kuma ƙanana yara 32.
Sakamakon harin dai, masu adawa da kasancewar Shugaba Bashar al-Assad kan karagar mulkin ƙasar sun sabunta kiraye-kiraye ga ƙasashen duniya na su afkawa mahukuntan Siriya da yaƙi kazalika 'yan adawar sun ce sun tsame hannunsu daga shirin na zaman lafiyar na Majalisar Ɗinkin Duniya har sai Majalisar Ɗinkin Duniyar ta tabbatar da tsaron rayukan fararen hular ƙasar.
Tuni dai madugun masu sanya idanun na Majalisar Ɗinkin Duniya Janar Robert Mood ya yi Allah wada da harin.
Shi ma dai ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya yi tur da harin inda ya ce su na nan su na gudanar da shiri don yin wani taro kan halin da Siriyan ke ciki.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi