1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Siriya sun ziyarci Haula inda aka kashe mutane 92

May 26, 2012

Masu sanya idanu na Majalisar Ɗinki Duniya kan shirin zaman lafiyar Siriya sun ziyarci wani waje da aka kai wani mummunan hari a ƙasar ta Siriya.

https://p.dw.com/p/1532Z
The bodies of people whom anti-government protesters say were killed by government security forces lie on the ground in Huola, near Homs May 26, 2012. The death toll has risen to at least 90 from Syrian shelling on the town of Houla on Friday, an opposition group said on Saturday. The UK-based Syrian Observatory for Human Rights said residents continued to flee the town, in central Homs province, in fear that artillery fire would resume. REUTERS/Shaam News Network/Handout (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Syrien Massaker in HuolaHoto: Reuters

Harin da aka kai daga tsakar ranar Juma'a zuwa asubahin yau asabar a garin Houla, ya yi sanadiyar rasuwar fararen hula 60 da kuma ƙanana yara 32.

Sakamakon harin dai, masu adawa da kasancewar Shugaba Bashar al-Assad kan karagar mulkin ƙasar sun sabunta kiraye-kiraye ga ƙasashen duniya na su afkawa mahukuntan Siriya da yaƙi kazalika 'yan adawar sun ce sun tsame hannunsu daga shirin na zaman lafiyar na Majalisar Ɗinkin Duniya har sai Majalisar Ɗinkin Duniyar ta tabbatar da tsaron rayukan fararen hular ƙasar.

Tuni dai madugun masu sanya idanun na Majalisar Ɗinkin Duniya Janar Robert Mood ya yi Allah wada da harin.

Shi ma dai ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya yi tur da harin inda ya ce su na nan su na gudanar da shiri don yin wani taro kan halin da Siriyan ke ciki.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi