1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jami'an agaji 192 sun halaka a zirin Gaza

November 8, 2023

Akalla jami'an agaji da na kiwon lafiya 192 sun halaka a zirin Gaza sakamakon luguden wutar da dakarun Isra'ila ke yi wa dan karamin yankin na Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4YXVb
Jami'an kiwon lafiya 192 sun mutu a Gaza
Jami'an kiwon lafiya 192 sun mutu a Gaza Hoto: Darrin Zammit Lupi/REUTERS

Kungiyar likitoci na gari na kowa Médecins Sans Frontières(MSF) ta sanar da mutuwar wani ma'aikacinta wanda aka kashe tare da wadansu 'yan uwansu a yayin wani harin bam da dakarun Isra'ila suka kai a sansanin 'yan gudun hijira na Chati da ke zirin Gaza.

Karin bayani: Asibitoci da dama sun rufe a Zirin Gaza

A cikin sanarwar da ta fidda, kungiyar ta nuna bacin rai kai yadda Isra'ila ta yi buris da kirayen-kirayen tsagaita buda wuta a Gaza abin da ta ce shine kadai hanyar kawo karshen kashe-kashen fararen hula da kuma ba da damar kai kayan agaji zirin.

Karin bayani: Yakin Gaza ya hallaka mata da kanana yara kusan dubu shida

A cewar ofishin hukumar kula da jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA akalla jami'an kiwon lafiya 192 aka kashe a Gaza tun bayan barkewar rikicin Isra'ila da Hamas, 14 daga cikinsu kuma sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suke bakin aiki.

Kawo yanzu dai a jimilce rikicin da ya barke a ranar bakwai ga watan Oktoba ya lakume rayukan akalla Falasdinawa 10,300 ciki har da kananan yara 4,237 kamar yadda sabin alkaluman mahukan Hamas suka nunar.