1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin malaman sakandare a Nijar

Issoufou Mamane LMJ
January 10, 2023

Sabuwar shekara ta 2023 na zaman wani kalubale ga hukumomi a Jamhuriyar Nijar, sakamakon yawan korafe-korafen kungiyoyin kwadago da ke dada karuwa a kasar.

https://p.dw.com/p/4Lyy0
Nijar l Mohamed Bazou | Malamai | Yajin Aiki
Gwamnatin Shugaba Mohamed Bazou na fuskantar kalubale daga malamaiHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Yajin aikin malaman koyarwa a Jamhuriyar Nijar da hadin gwiwar wasu kungiyoyin malaman koyarwa na sakandare masu yi wa kasa hidima ta kwantaragi, ya dauki matakin dakatar da da aiki na wa'adin kwanaki hudu. Hadin gwiwar kungiyoyin malaman koyarwar na sakandare, sun ajiye takardar tsunduma yajin aikin daga Larabar wannan makon ya zuwa Asabar din karshen mako. Matakin kaurace wa ajujuwa na kwanaki hudun dai, na zuwa ne sakamakon abin da malaman suka ce rashin cika alkawuran da gwamnatin ta yi na daukar malaman koyarwar a matakin din-din-din da wasu alawus-alawus da suka makale har tsawon sama da shekaru biyar. A kwanankin baya baya dai, gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar ta fitar da wata takarda ta daukar malaman. Saidai a nasu bangaren malaman makarantun sun yi watsi da ita, suna zargin gwamnatin da nuna son rai da siyasa a sha'anin.