1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadun MDD sun kadu da abin da suka gani a Rafah

Abdullahi Tanko Bala
December 11, 2023

Jakadun kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da suka ziyarci iyakar Rafah sun baiyana damuwa da halin tagaiyarar al'umma a Gaza.

https://p.dw.com/p/4a2jK
Nahostkonflikt - Rafah
Hoto: Mohammed Abed/AFP

Jakadun kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya  sun baiyana matukar damuwa game da halin tagaiyarar al'umma a Gaza. Jakadun sun baiyana hakan ne yayin ziyarar da suka kai mashigin Rafah da ke iyaka da kudancin Gaza

Ziyarar na zuwa yan kwanaki bayan da Amurka ta hau kan kujerar na ki kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya na neman tsagaita wuta.

Ziyarar ta kwana guda kasar Hadaddiyar daular laraba da kuma Masar suka shiryata yayin da ake ci gaba da fuskantar matsanancin halin rayuwar al'umma a Gaza da yaki ya daidaita, yankin da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya baiyana da cewa ya zama tamkar makabarta.

Jakadu daga kasashe da dama da suka hada da Rasha da Birtaniya na daga cikin ayarin da suka kai ziyarar. Sai dai  Amurka wadda ta  hau kujerar na ki akan kudirin tsagaita ba ta tura wakili ba a ziyarar haka ma kasar Faransa.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Masar ya shaidawa jakadun cewa babu wata hujja da za ta sa a kau da kai daga ukubar da ake gana wa al'ummar Falasdinawa a Gaza.