Jakadan Siriya ya yi sauyin sheƙa
July 12, 2012Jakadan Syria a Iraki, Nawaf Fares yayi sauyin sheƙa zuwa ɓangaren 'yan adawa, tare da kira ga sojojin ƙasar da su juya bakin bingigarsu zuwa kan gwamnati. Wannan dai shine babban jami'in gwamnatin Bashar al-Assad na farko, da ya juya wa gwamnatin na siriya baya. A sakon da kafafen yaɗa labarai suka gabatar, Fares yace ya janye daga jam'iyyar da ke mulki ta Baath tare da barin mukaminsa a matsayin jakadan gwamnati. Kazalika ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga sauran 'yan jam'iyyar Baath dake mulki, da su yi watsi da gwamnatin Bashar al-Assad.
Majiyar diplomasiyya ta shaidar da cewar, tuni jami'in diplomasiyyan na Siriya ya mika wasikarsa ta barin aiki wa magabatan Iraki, kuma wani lokaci a yau ne zai gana da magabatan na Iraki.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umar Saleh Umar