1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Jagoran adawa ya fita hayyacinsa

October 25, 2023

Rahotanni daga Senegal na nuni da cewa an kwantar da babban jagoran adawa Ousmane Sonko da ya koma yajin cin abinci kwanaki takwas din da suka gabata, a sashen kula da marasa lafiyar da suka fita hayyacinsu wato ICU.

https://p.dw.com/p/4Y263
Senegal I Jagoran 'yan adawa Ousmane Sonko
Ousmane Sonko jagoran 'yan adawa na kasar SenegalHoto: Seyllou/AFP

Guda daga cikin lauyoyin babban jagoran adawar na Senegal Ousmane Sonko ne ya shaida hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, inda ya ce dan siyasar ya fita cikin hayyacinsa ne a ranar 23 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki kwana guda bayan ya yi magana da shi. Koda yake lauyan ya bayyana cewa Sonko ya dawo cikin hayyacinsa tun a ranar, sai dai kuma jikinsa ya yi tsanani sosai.